Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Bangarorin biyu sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasa da kasa musamman rikicin Ukraine.
Sun kuma tattauna batun kare ofisoshin diflomatsiyya da aikewa da tallafin jin kai dama batutuwan da suka shafe alakar dake tsakaninsu.
Iran ta bakin ministan harkokin wajenta ta ce tana goyan bayan duk wani yunkuri na shawo kan rikice rikice a duniya, musamman a Ukraine, Afganistan, Yamen da ma wasu kasashe ba tare da siyasa mai harshen damo ba, a cewar Amir Abdollahian.
A wani labarin kuma ministan harkokin wajen kasar ta Iran, zai isa birnin Moscow na kasar Rasha a wannan Talata, domin tattauna batutuwan da suka shafi yankin dama yarjejeniyar nukiliyar Iran.
342/